Gwamna Ya Ziyarci Wurin da Jirgin Sojoji Ya Jefa Bama-Bamai kan Bayin Allah
Sokoto – Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya ziyarci garuruwa biyu da jiragen yakin sojoji suka yi musu luguden bama-bamai bisa kuskure. Akalla mutane 10 ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama a wani hari ta sama da ake zargin sojoji sun kai kan fararen hula a safiyar yau Laraba. >>>